Bayern Munich da PSG za su iya murnar lashe lig dinsu na gida a wannan makon

.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Bayern Munich da Paris St-Germain dukkansu za su iya yin murnar daukar kofi a wannan makon
An wallafa

An cire Bayern Munich da Paris St-Germain daga Chmapions Lig, amma dukkansu za su iya murnar lashe kofinsu na gida a karshen wannan makon da muke ciki.

Haka abin yake a Sifaniya ma, Real Madrid za ta iya lashe La Liga kuma tana da damar lashe Champions, yayin da a Italiya har yanzu da sauran runa a kaba.

BBC ta yi duba kan abubuwan da za su iya faruwa a manyan gasannin Turai hudu a karshen wannan makon.

Ko Bayern za ta iya samun nasara a wasan Der Klassiker su kuma ci Bundesliga?

Manyan wasannin da za a buga a karshen wannan makon, wasan da za a yi a Jamus na ciki na da Der Klassiker.

Wasa tsakanin Bayern Munich da Borussia Dortmund na daga cikin manyan wasanni a ko wanne irin yanayi. A yau Asabar kuma za su fafata da misalin karfe (17:30).

Bayern na kan hanyar lashe gasar Bundesliga karo na 10 a jere, kuma za su iya hada maki na tara tsakaninsu da Dortmund yayin da ya rage wasa hudu kacal a kammala gasar.

Babu abin da Dortmund ke fata irin ta janyo wa Bayern Munich jinkirin murnar cin kofin a filin wasa na Allianz Arena.

Robert Lewandowski celebrates scoring for Bayern Munich

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Robert Lewandowski ya ci kwallo 32 a gasar Bundesliga a wannan kakar

Nasarar da masu masaukin baki za su yi za su yi ta ne tare da murnar daukar kofi. Kocin kungiyar Julian Nagelsmann wanda ya amshi kungiyar a bara, a makon da ya wuce ne yace an rika yi masa barazanar rayuwarsa a intanet bayan fitar da ita da aka yi daga Champions.

"Nasan kofin gida ba wani mahimmanci ne da shi ba sosai a wajen Munich," Julian Nagelsmann ya ce. "Amma duk da haka abu ne mai kyau."

PSG na tunkarar kofi na 10?

Bayan kammala wasa da maki daya da ke tsakaninta da Lille gwarzuwar gasae bara, PSG za ta ci lig na 10 a jere tare da cewa suna da wasa hudu a hannu, dole kuma su yi abin da za su ci wasansu da Lens a ranar Asabar 20:00.

Zai zama karon farko da tsohon kocin Tottenham Mauricio Pochettino zai ci kofi a Faransa tun bayan barin Thomas Tuchel a watan Janairun 2021.

An rika alakanta Pochettino da Manchester United, wadda ta sanar da daukar Erik ten Hag a matsayin sabon kocinta.

"Zai zama abin farin ciki in kasance cikin wadanda tarihin kungiyar da ta ci kofi 10," in ji kocin Argentina.

Paris St-Germain boss Mauricio Pochettino

Asalin hoton, Reuters

PSG za su buga wasan ne yayin da suke da maki 77 cikin wasa 33, - tazarar maki 15 tsakaninta da Marseille lokanin da ya rage wasa biyar a kammala wasanni.

Lens suna matsayi na bwakai a gasar, kuma suna fatan shiga cikin kungiyoyi uku da za su halarci gasar Champions mai zuwa.

Haka kuma ba za a bar magoya bayan Lens su je Paris ba saboda tsoron hayaniya.

Real Madrid na tsaka mai wuya

A Sifaniya, masu jan ragamar La Liga Real Madrid ba za su yi wannan wasan a wannan makon ba, saboda su samu damar shirya wa wasan Champions na ranar Talata da za su yi da Manchester City.

Shi kuma kocin kungiyar Carlo Anceloti ya samu nasarar cin La Liga ko da bai jefa kwallo guda ba.

Real Madrid na saman Barcelona da maki 15 da take matsayi na biyu, wadanda za su yi wasansu da Rayo Vallecano a ranar Lahadi.

Real Madrid boss Carlo Ancelotti

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Carlo Ancelotti na aiki ne a karo na biyu wajen horar da Real Madrid

In Barcelona ta yi rashin nasara Real Madrid za ta nemi maki daya ne kacal a wasannin biyar da suka yi ragowa domin cin lig na 35 a tarihi.

Akwai sauran runa a kaba a Serie A

Abin a matse yake a Italiya, yayin AC MIlan da ke saman tebur za ta buga wasanta na wannan makon da tazarar maki biyu kacal.

Kazalika, Inter Milan na da kwantan wasa daya, yayin da Napoli suke da maki hudu da kuma wasa biyar a hannu.

AC Milan's Olivier Giroud celebrates scoring

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Olivier Giroud ya ci kwallo takwas a AC Milan a lig tun bayan komawarsa kungiyar a watan Yulin bara

Inter za su koma matsayi na daya idan suka ci wasan da za su buga da Roma da ke matsayi na biyar, yayin da AC ba za ta yi wasa ba sai rnaar Lahadi da Lazio da ke matsayi na bakwai.

"Mun san akwai sauran watanni da kuma wasanni masu zafi," in ji kocin Inter Simone Inzaghi.

Rabon da AC MIlan ta ci Serie A tun 2010-11.