Liverpool 3-3 Benfica: Ko Liverpool na hanyar lashe kofi hudu a bana?

An wallafa

Liverpool na shirin lashe kofi hudu a kakar bana, bayan da ta fitar da Benfica daga Champions League duk da tashi 3-3 da suka yi a Anfield ranar Laraba.

Liverpool ta kai zagayen daf da karshe da ci 6-4 gida da waje, bayan da ta doke Benfica 3-1 a wasan farko a kwata fainal ranar Talata 5 ga watan Afirilu a Portugal.

Wadanda suka ci wa Liverpool kwallayen a Ingila sun hada da Ibrahima Konate da kuma Roberto Firmino da ya zura biyu a raga.

Benfica kuwa ta zura kwallayen ta hannun Goncalo Ramos da Roman Yaremchuk da kuma Darwin Nunez.

Da wannan nasarar da kungiyar Anfield ta yi za ta fafata da Villareal a wasan daf da karshe a Champions League ranar 26 ga watan Afirilu a Ingila, sannan suyi wasa na biyu ranar 4 ga watan Mayu a Sifaniya.

Liverpool wadda ke fatan lashe kofi hudu a bana, bayan da ta dauki Caraboa Cup za ta buga daf da karshe ranar Asabar da Manchester City a FA Cup.

Kungiyoyin biyu sun tashi 2-2 ranar Lahadi a gasar Premier League, inda City ke jan ragamar teburin babbar gasar tamaula ta Ingila da tazarar maki daya tsakaninta da Liverpool ta biyu.