Liverpool ta shiga cikin hudun farko a Premier League

An wallafa

Ranar Laraba Liverpool ta yi nasarar doke Burnley da ci 3-0 a wasan mako na 37 da suka fafata a gasar Premier a Turf Moor.

Liverpool ta ci kwalln farko ta hannun Roberto Firminho sauran minti biyu su je hutun rabin lokaci.

Yayin da Nathaniel Phillips ya ci wa kungiyar Anfield kwallo na biyu ana tsaka da wasa a zagaye na biyun.

Liverpool ta ci na uku ne ta hannun Alex Oxlade-Chamberlain saura minti biyu a tashi daga fafatawar

Da wannan sakamakon Liverpool ta zama ta hudu a kan teburi da maki 66 iri daya da na Leicester City wadda ta koma ta biyar kawo yanzu.

Chelsea ce a mataki na uku mai maki 67 da tazarar maki hudu tsakaninta da Manchester United ta biyu.

Ita kuwa Burnley ta yi kasa zuwa mataki na 17 a kasan teburi da maki 39, bayan da tuni Fulham da West Brom da kuma Sheffield United za su buga Championship a badi.

Wasannin karshe a Premier da za a buga ranar 23 ga watan Mayu:

  • Arsenal da Brighton & Hove Albion
  • Aston Villa da Chelsea
  • Fulham da Newcastle United
  • Leeds United da West Bromwich Albion
  • Liverpool da Crystal Palace
  • Manchester City da Everton
  • West Ham United da Southampton
  • Leicester City da Tottenham
  • Sheffield United da Burnley
  • Wolverhampton Wanderers da Manchester United