Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Brazil da Senegal sun buga kunnen doki
Tawagar kwallon kafa ta Brazil ta tashi 1-1 da ta Senegal a wasan sada zumunta da suka yi ranar Alhamis a Singapore.
Dan wasan Liverpool, Roberto Firminho ne ya fara ci wa Brazil kwallo, bayan da Gabriel Jesus ya ba shi tamaula.
Ita kuwa Senegal ta farke ne ta hannun Famara Diedhiou a bugun fenariti, bayan da aka yi wa Sadio Mane keta a da'ira ta 18.
A karawar ce Neymar ya buga wa tawagar kwallon kafa ta Brazil wasa 100, kuma an ba shi riga mai lamba 100 tun kan fara fafatawar.
Sau biyu Neymar ya kusan cin kwallo a bugun tazara, inda ta farko ta fada saman raga ta biyu kuwa mai tsaron raga Alfred Gomis ne ya ture ta.
Ita ma Senegal ta kai hare-hare da dama musamman wadda dan wasan Liverpool, Sadio Mane ya buga kwallo ya bugi turke.
Brazil za ta buga wani wasan sada zumunta da tawagar kwallon kafar Najeria ranar 13 ga watan Oktoba a Singapore.
Wannan ne karo na biyu da tawagogin biyu za su fafatawa, tun bayan 2003 inda Brazil ta yi nasara da ci 3-0 a Abuja.
Brazil ce ta lashe Copa America da ta karbi bakuncin wasannin, ita kuwa Najeriya ce ta yi ta uku a gasar kofin nahiyar Afirka da aka yi a Masar.