Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Pogba, Kane, Mbappe, Zaha, Nunez, da Phil Foden

Asalin hoton, Getty Images
Paris St-Germain ta yi wa dan wasan tsakiya na Faransa Paul Pogba, mai shekara 29, ta yi, a daidai lokacin da ya shiga watan shi na karshe a kwantiragi da Manchester United, sai dai kungiyar ta Ligue 1 ta yi tayin kudin da bai kai na United ba. (MEN)
Real Madrid na da kwarin gwiwar za ta rattaba hannu kan yarjejeniyar dauko dan wasan gaba na Faransa Kylian Mbappe mai shekara 23, daga PSG a kakar wasannan, duk da fadi-tashin da yake yi na ganin ya sabunta zamansa a kungiyar. (90min)
Dan wasan Tottenham, mai kai hari na Ingila Harry Kane, mai shekara 28, na tsaka-mai-wuyar sauraron tayin Manchester United a kakar wasan bana, kafin ya yanke shawarar tsawaita zama a kungiyar. (The Athletic - subscription required)
Crystal Palace kuwa na jiran tayin dan wasan gaba na Ivory Coast Wilfried Zaha, mai shekara 29. (Mail)
Dan wasan gaba na Wales Gareth Bale, mai shekara 32, zai bar Real Madrid a karshen kakar wasan da muke ciki, sai dai babu wani mataki da aka dauka kan makomarsa nan gaba, kamar yadda wakilinsa ya bayyana. (Deportes Cuatro, via Mirror)
Manchester United da Atletico Madrid na daga cikin kungiyoyin da ke fatan samun dama kan dan wasan Benfica mai shekara 22, mai kai hari na Uruguay wato Darwin Nunez. (Telegraph - subscription required)
Liverpool ta shirya domin rufe sabbin kwantiragi uku da suka rattabawa hannu. Tuni suka cimma yarjejeniya da matasan 'yan wasa masu jini a jika, kamar dan wasanFulham asalin Portugal, kuma dan wasan tsakiya Fabio Carvalho, mai shekara 19, dan dan wasan Celtic winger Ben Doak, mai shekara16, da dan wasan City Derry mai shekara 15 da Trent Kone-Doherty. (Football Insider)

Asalin hoton, Getty Images
Manchester City na fatan cimma yarjejeniya da dan wasan tsakiya na Ingila, mai shekara 21 Phil Foden kafin karshen kakar bana. (90min)
Ta yiwu tabbatar da Erik ten Hag a matsayin manajan Manchester United, za ta sanya a ga matashin dan wasa mai shekara 20 mai tsaron gida dan Denmark Jurrien Timber da dan Brazil mai shekara 22 winger Antony daga Ajax a kakar wasan bana. (Mike Verweij, via Express)
Manajan riko a United Ralf Rangnick ka iya amfani da kwantiraginsa na RB Leipzig domin dauko dan wasan tsakiya na Australia Konrad Laimer, mai shekara 24, zuwa Old Trafford. (Bild, via Express)
Manchester Unitedna neman sabon manaja, tsakanin kocin Ajax Ten Hagda naPSG Mauricio Pochettino. (The National)
Newcastle United ta bude kofar sayar da dan wasan gaba na Faransa Allan Saint-Maximin, mai shekara 25, a bazara. (90min)










