Karim Benzema ya kara yaga barakar Chelsea

An wallafa

Real Madrid ta je da doki Chelsea da ci 3-1 a wasan quarter finals zagayen farko da suka kara ranar Laraba.

Real ta fara cin kwallo ta hannun Karim Benzema a minti na 12 da fara wasa, sannan dan kwallon Faransa ya kar na biyu a wasan.

Chelsea ta farke ta hannun Kai Havertz saura minti biyar su je hutu, daga baya Benzema ya kara na uku a karawar.

Da wannan sakamakon Benzema ya zama na farko da ya ci Chelsea kwallo uku rigis a Champions League.

Haka kuma dan wasan ya zama na farko daga Faransa da ya ci kwallo 10 ko fiye da haka a kaka daya a Champions League.

Dan wasan Real Madrid, David Alaba ya buga gumurzun, kuma na 100 a Champions League na farko daga Austria da ya yi wannan bajintar.

Kuma cikin wasa 100 da ya yi a gasar kofin zakarun an ci karawa 67 da shi a fafatawar da ya yi wa Bayern Munich da Real Madrid.

Wannan shine karon farko da Real Madrid ta doke Chelsea mai rike da Champions League a karawa shidan da suka yi a kofin Zakarun Turai.

Chelsea ta yi nasara a uku, Real ta ci daya da canjaras biyu.

Ko a bara Chelsea ce ta yi da Real Madrid a Champions League daga baya ta hadu da Manchester City ta lashe kofin.

Chelsea ta karbi bakuncin Real Madrid a lokacin da ta sha kashi a hannun Brentford da ci 4-1 a gasar Premier League ranar Asabar.

Chelsea wadda aka ci kwallo bakwai a wasa biyu a jere, za ta ziyarci Southampton ranar Asabar a gasar Premier League.

Ita kuwa Real Madrid wadda ke jan ragamar teburin La Liga za ta karbi bakuncin Getafe ranar Asabar.