Watakila a sayar da Chelsea nan da karshen watan nan

Asalin hoton, Getty Images
Wani kamfanin Amurka da aka bai wa alhakin sayar da Chelsea ya ce yana sa ran nan da karshen watan nan za a kammala cinikin kungiyar.
Hakan ya biyo bayan karfin gwiwa da ya samu daga gwamnatin Burtaniya, bayan da suka tattauna a tsakaninsu.
Gwamnatin na bukatar gyare-gyaren lasisin kungiyar kan a sayar da Chelsea, bayan da aka dora wa mamallaki Roman Abramovich takunkumi a makon jiya.
An cimma matsaya cewar gwamnatin Burtaniya ce za ta bayar da izinin sayar da Chelsea kuma kudin cinikin za a zuba a gidauniyar taimakawa wadanda yakin da ake yi a Ukraine ya shafa.
Gwamnatin Burtaniya ta samar da wani lasisi na musamman domin bai wa Chelsea damar ci gaba da gudanar da ita, bayan da aka rufe asusun Abramovich, wanda ake alakanta shi da shugaban Rasha, Vladimir Putin.
A sabon tsarin lasisin da gwamnati ta samar, ba damar a sayar da Chelsea har sai ta bayar da izini.
An dage wa'adin cimma yarjejeniyar sayar da kungiyar zuwa ranar Juma'a 18 ga watan Maris, inda sama da mutum 20 ke son mallakar kungiyar.
Chelsea mai rike da Champions League za ta je gidan Lille ranar Laraba a karawar daf da na kusa da na karshe, kuma kungiyar Stamford Bridge ce ta yi nasara da ci 2-0 a wasan farko.











