Arsenal 2-0 Leicester City: Gunners ta ci wasa na biyar a jere a Premier

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal ta koma mataki na hudu a kan teburin Premier League, bayan da ta doke Leicester City 2-0 ranar Lahadi a Emirates.
Wasa na biyar kenan a jere da Arsenal ta ci a gasar Premier League a kokarin da take na samun gurbin buga Champions League a kakar badi.
Thomas Partey ne ya fara ci wa Gunners kwallo, daga baya Alexandre Lacazette ya kara na biyu a bugun daga kai sai mai tsaron raga.
Da wannan sakamakon Arsenal ta koma ta hudu a kan teburin kakar bana da tazarar maki daya tsakaninta da Manchester United, wadda ta doke Tottenham ranar Asabar.
Leicester City wadda ta sha kashi a Emirates karkashin koci Brendan Rodgers ta ci gaba da zama ta 12 a teburin Premier League.
Arsenal wadda rabon da ta buga Champions League tun bayan kaka biyar ta ci gaba da taka rawar gani a bana, bayan da ta yi nasara a wasa tara daga 11 da ta buga a bayan nan a Premier League.
Gunners wadda take da kwantan wasa uku na sa ran yin abin a zo a gani, domin ta samu buga Champions League a badi, kuma ranar Laraba Arsenal za ta fafata da Liverpool wadda ta ci 4-0 a wasan farko a bana a Anfield.
Ita kuwa Leicester City za ta buga gasar Turai ta European Conference League karawar daf da na kusa da na karshe da Rennes ranar Alhamis.










