Marcelo Bielsa: Leeds United ta kori kocinta bayan kashin da ta sha hannun Tottenham

Marcelo Bielsa

Asalin hoton, Reuters

An wallafa

Leeds United ta kori kocinta Marcelo Bielsa bayan abubuwa sun taɓarɓare.

Kocin ɗan ƙasar Argentina mai shekara 66 ya karɓi aikin horar da Leed ne a watan Yunin 2018, kuma yanzu ƙungiyar na zaune maki biyu tsakaninta da ƙasan tebur.

A bara ƙarƙashin jagorancin Bielsa Leeds ta kammala kaka a matsayi na tara, shekarar da ta hauro gasar Premier bayan shafe shekara 16 ba ta gasar.

Amma kashin da Leeds ta sha 4-0 a hannun Tottenham, na nufin ta sha kashi wasa hudu a jere.

Shugaban Leeds Andrea Radrizzani ya ce sun yanke shawarar yanke ƙauna da kocin ne saboda yadda abubuwa suka taɓarɓare.

"Mun samu kanmu a matsayi marar kyau, kuma ina ganin yanzu lokaci ne da ya kamata mu kawo sabon koci domin ya yi tasiri a wannan lokaci na wannan kaka mafi ƙalubale," in ji Radrizzani.

A mako mai zuwa Leeds United za ta ziyarci Leicester City wasan mako na 28 na gasar Premier League.