Carabao Cup: Wa zai kafa tarihi a Wembley tsakanin Tuchel da Klopp

Tuchel v Klopp

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Chelsea da Liverpool za su hadu a wasan karshe na kofin Carabao a filin Wembley, don sanin wanda zai fara lashe kofin gida na farko a 2022.

Masu horar da kungiyoyin Thomas Tuchel da Jurgen Klopp sun taba lashe kofuna a gasar Zakarun Turai, to amma babu wanda ya taba lashe irin wannan kofi a cikin su.

Rabon Chelsea da lashe Carabao Cup tun a shekarar 2015, ita kuwa Liverpool shekaru 10 kenan rabonta da shi.

Kuma wannan ne karon farko da za a samu wata kungiya ta daban da za ta lashe kofin, don tun a shekarar 2017 Manchester City ke lashe kofin, in ban da bana da West Ham ta cire ta.

Liverpool na da damar lashe kofuna hudu a bana farawa da kofin na Carabao, sai dai Chelsea tuni ta dauki biyu ta na neman na uku.

Ba a jima ba da Chelsea ta dauki kofin zakarun turai na Super Cup, ta kuma hada da na zakarun kungiyoyin duniya wato Club World Cup.

A cewar Jurgen Klopp kungiyarsa ta yi amfani da yan wasa a matakan matasa yan 18 da 23 kafin su kawo wannan mataki, saboda haka yana da kwarin gwuiwar cewa za su iya taka rawa su kuma kafa tarihi a wasan na yau.

Keheller

Asalin hoton, Getty Images

Daya daga cikinsu shine mai tsaron raga Caoimhin Kelleher, wanda ake sa ran a yau ma shi zai kama wa Liverpool raga a maimakon Allison Becker.

" Yana da kyau a mayar wa matashin mai tsaron raga da biki, ba abun mamaki bane shi zai kama wasan na yau.'' In ji mataimakin kocin Liverpool Pep Lijnders.

A bangaren Chelsea ma abun haka yake, don Kepa Arrizabalaga ne ya kama wasannin Chelsea na Carabao tun da aka fara a maimakon Edouard Mendy.

Kuma Tuchel ya fadi cewa dan kasar Sfaniyar '' ya yi matukar cancantar ya kama a yau'', duk da kulob din bai tabbatar da cewa shi din ne zai shiga raga ba a filin na Wembley.