Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Serie A: An dakatar da Mourinho wasanni biyu bayan rikici da lafari
An dakatar da kocin Roma Jose Mourinho wasanni biyu, bayan da aka bashi jan kati a wasan Serie A da suka yi da Verona ranar Talata.
Mourinho ya yi wa alkalin wasa Luca Pairetto fada, wanda hakan yasa ya bashi jan kati a wasan wanda aka tashi 2-2.
Kafafen cikin gida sun ce Mourinho ya yi fada ne da cewa lokacin da aka kara a wasan ya yi kadan.
A yanzu Roma na kasan Juventus wadda ita ce ke zaune a na hudu da tazarar maki shida.
Mourinho bai tsaya ga fada ba kawai, sai da ta kai ga ya dauki kwallo ya buga sama saboda yadda ya fusata.
Bugu da kari ya ki halartar hira da manema labarai, inda ya rubuta a shafinsa na Instagram cewa '' na zabi na je gida in ci abincin dare cikin natsuwa.''
Bayan dakatarwar an ci kocin na Roma tarar yuro 20,000.
Shima janar manaja na Roma Tiago Pinto an dakatar da shi har zuwa 8 ga watan Maris saboda zargin alkalin wasan, to amma an yi masa sassauci bayan da ya bada hakuri.
Ko a 2010 da Mourinho na Inter Milan ya taba inkiya ya nuna wa alkalin wasa cewa za a daure shi, wanda hakan yasa aka dakatar da shi wasanni uku.