Afcon 2021: Senegal ta tsallaka zagayen gaba bayan doke Cape Verde

Asalin hoton, Getty Images
Senegal ta kai wasan semi fayinal bayan ta doke tawagar ƙwallon ƙafa ta Cape Verde 2-0 a wasan zagayen 'yan 16 a gasar Kofin Ƙasashen Afirka da ke gudana a Kamaru.
Tauraron ɗan wasa Sadio Mane ne ya fara zira ƙwallo a ragar Cape Verde jim kaɗan bayan an bai wa mai tsaron raga Vozinha jan kati sakamakon karon da suka yi da ɗan wasan na Liverpool.
Mane ya ci gaba da wasan duk da kaɗuwar da ya yi bayan karon, sai dai bai ci gaba da wasan ba, inda Ahmadou Bamba Dieng ya karɓe shi a minti na 70.
Ana cikin ƙarin lokaci ne kuma Dieng ya ƙara ta biyu.

Asalin hoton, Getty Images
Senegal za ta kara da ƙungiyar da ta yi nasara a wasan Malawi da Morocco, wanda za a take da ƙrfe 8:00 agogon Najeriya.
Senegal ta lashe wasanninta huɗu da ta buga a zagayen kwab ɗaya a baya, amma Algeria ce ta doke ta a gasar 2019.
Fitaccen ɗan wasan Senegal da Liverpool Sadio Mane, ya taka rawa a kusan kashi 50 na ƙwallayen da Senegal ta yi nasara tun daga gasar Afcon ta 2017, inda ya ci ƙwallo shida tare da taimakawa a ci.
Karo na biyu kenan da Cape Verde ta buga zagayen kwab ɗaya. Ghana ce ta fitar da ita a gasar ta 2013 a zagayen semi fayinal.
Morocco da Malawi

Asalin hoton, Caf
Tawagar Atlas Lions ta Morocco za ta fafata da tawagar Malawi a ranar Talata a Yaounde, zagaye na biyu na gasar cin kofin Afirka.
Karon farko kenan da Morocco za ta hadu da Malawi a gasar cin kofin Afirka.
Sau ɗaya Morocco ta yi rashin nasara a haɗuwa 11 da ta yi da sabbin ƙasashe inda ta ci bakwai ta yi kunnen doki uku, yayin da kuma Gabon ta doke ta 3-2 a gasar 2012.
Karon farko kenan da Malawi za ta buga wasan zagaye na biyu a gasar cin kofin Afirka, kuma wasa na 10 da za ta buga a gasar.
Duk ƙasar da ta yi nasara za ta haɗu da Senegal ko Cape Varde.









