Afcon 2021: Wa zai kai zagayen gaba tsakanin Burkina Faso da Gabon?

Burkina Faso

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Ranar Lahadi za a fara wasan zagaye na biyu a gasar cin kofin Afirka, inda za a kece raini tsakanin Burkina Faso da Gabon a karawar da za su yi a Limbe.

Rana: 22 January 2022

Lokaci: 17:00 agogon Kamaru (16:00 GMT)

Wuri : Limbe Stadium, Limbe

Tun daga 2003 tawagogin sun fafata sau tara a tsakaninsu a dukkan haduwa, inda Gabon ta ci wasa uku da canajaras hudu, yayin da Burkina Faso ta yi nasara a biyu.

Burkina Faso ta yi rashin nasara a wasa daya daga tara baya da ta yi, wadda ta ci hudu da canjaras hudu.

Gabon ba ta yi rashin nasara ba a wasa shida baya a Afcon mai nasara daya da canajaras biyar, koda yake wasa daya ta ci a fafatawa takwas da canjaras biyar da rashin nasara biyu, tun bayan da ta doke Burkina Faso 2-0 a 2015.

Idan Burkina Faso ta yi nasara za ta kai quarter finals kenan karo na uku a gasa hudu a Afcon, wadda ta yi ta hudu a 1998.

Wasannin da suka buga a tsakaninsu:

Wasan sada zumunta 2 ga watan Janairu 2022

  • Burkina Faso 3 - 0 Gabon

Gasar kofin Afirka 18 ga watan Yunin 2017

  • Gabon 1 - 1 Burkina Faso

Gasar kofin Afirka 17 ga watan Junin 2015

  • Burkina Faso 0 - 2 Gabon

Gasar kofin Afirka 15 ga watan Oktoban 2014

  • Burkina Faso 1 - 1 Gabon

Gasar kofin Afirka 11 ga watan Oktoba 2014

  • Gabon 2 - 0 Burkina Faso

Wasan shiga gasar kofin duniya 7 ga watan Satumba 2013

  • Burkina Faso 1 - 0 Gabon

Wasan shiga gasar kofin duniya 9 ga watan Yunin 2012

  • Gabon 1 - 0 Burkina Faso

Wasan sada zumunta 9 ga watan Yunin 2012

  • Gabon 0 - 0 Burkina Faso

Wasan sada zumunta 8 ga watan Nuwamba 2003

  • Gabon 0 - 0 Burkina Faso