Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Afcon 2022: Najeriya ta doke Sudan 3-1 a wasa na biyu a rukuni na hudu
Kafar tawagar Nageriya daya ta kai zagaye na biyu a gasar cin kofin Afirca, bayan da ta doke Sudan 3-1 a wasa na biyu a cikin rukuni na hudu ranar Asabar.
Super Eagles ta ci kwallo biyu tun kan hutu ta hannun 'Samuel Chukwueze da kuma Taiwo Awoniyi.
Bayan da suka koma karawar zagaye na biyu Nageriya ta kara na uku ta hannun Moses Simon.
Sudan ta zare daya a bugun daga kai sai mai tsaron raga ta hannun Walieldin Khidir.
Da wannan sakamakon Super Eagles wadda ta doke Masar da ci 1-0 ranar Talata ta hada maki shida a wasa biyu tana jan ragamar teburi na hudun.
Ita kuwa Sudan maki daya ne da ita, bayan wasa biyu, za kuma a kara a fafatawa ta biyu tsakanin Guinea Bissau da Masar a Garoua.
Ranar Laraba za a buga wasa na uku na cikin rukuni na uku tsakanin Masar da Sudan da na Najeriya da Guinea Bissau.
Guinea Bissau da Masar
Guinea Bissau tana da maki daya, bayan da ta tashi 0-0 tsakaninta da Sudan a wasan farko na cikin rukuni.
A kuma ranar ce Masar ta yi rashin nasara a hannun Nageeriya a karawar farko ta cikin rukuni na hudu a Garoua.
Rana: 15 Janairu 2022
Lokaci: 20:00 agogon Kamaru (19:00 GMT)
Fili: Roumde Adjia, Garoua
Karawa tsakanin Guinea-Bissau da Masar
Wannan shine wasan farko da za a buga tsakanin Guinea-Bissau da Masar a gasar cin kofin nahiyar Afirka.
Har yanzu Guinea-Bissau ba ta ci wasa ba karawa bakwai a Afcon, mai canjaras uku da shan kashi a wasa hudu.
Za kuma ta iya zama ta bakawi da suka yi karawa takwas ba tare da yin nasara ba, bayan tawagar Angola da Benin da Kenya da Mozambique da Namibia da kuma Uganda.
Masar ta taba kasa cin wasa biyu a jere a karon farko a Afcon a 2002.
Guinea Bissau ta kasa zura kwallo a raga a wasa biyar a jere a Afcon, wadda ta yi karawa shida ba tare da cin kwallo ba itace Kenya a 1990.