Barcelona 2-3 Real Madrid: Real ta kai wasan karshe a Spanish Super Cup

Real Madrid celebrate

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Real Madrid na fatan lashe Spanish Super Cup na 12 jumulla
An wallafa

Real Madrid ta kai zagayen karshe a Spanish Super Cup, bayan da ta doke Barcelona 3-2 a ranar Laraba a Saudi Arabia.

A karawar ta hamayya ta El Clasico, Federico Valverde ne ya kai Real Madrid wasan karshe, wanda ya ci kwallo na uku a karin lokaci.

Real ce fara jefa kwallo ta hannun Vinicius Junior a minti na 25 da take leda, sai dai kuma daf da za su je hutu Barcelona ta farke ta hannun Luuk de Jong.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Karim Benzema ya ci na biyu, Ansu Fati ya farke da ta kai aka je karin lokaci, inda Real Madrid ta yi nasara.

Karo na biyu kenan da Real ta ci Barcelona a kakar bana, bayan da a gasar La Liga ta yi nasara da ci 2-1 ranar 24 ga watan Oktoban 2021.

Sabon dan kwallon da Barcelona ta dauka daga Manchester City ya buga mata karawar a Saudi Arabia, amma bai ci kwallo ba, an kuma sauya shi a zagaye na biyu.

Ranar Alhamis za a buga daya wasan na daf da karshe tsakanin Atletico Madrid da Athletic Bilbao.

Za a buga wasan karshe da duk wadda ta yi nasara Real Madrid ranar 16 ga watan Janairu a King Fahd International Stadium