Afcon 2021: Yadda Kamaru ke shirin karawa da Ethiopia

Kamaru
An wallafa

Kamaru na shirin haduwa da Ethiopia a gasar Kofin Ƙasashen Afirka a karawa ta biyu a rukuninsu na farko.

Kamaru

Rukunin nasu ya kunshi Kamaru da ake buga gasar a kasarta, da Ethiopia da Burkina Faso da Cape Varde, waɗanda za su yi karawa zagaye na biyu a rukuninsu a birnin aounde.

Kamaru da ta doke Burkina Faso ci 2-1 a wasan Farko.

Kamaru

Karo na biyu kenan da kasashen biyu za su hadu a gasar da ake yi wa lkabi da Afcon 2021 tun haduwar da suka yi a 1970, inda Kamaru ta yi nasara ci 3-2.

Kamaru

Kamaru na harin cinye wasanninta biyu a jere kamar yadda ta taba yi a gasar 2006.

Idan har Kamaru ta yi nasara zai kasance tana da maki shida kuma ta tsallake zuwa zagaye na gaba kafin ta buga wasa da Cape Varde wadda ta samu nasara kan Ethiopia a wasansu na farko.