Afcon 2021: Hotunan yadda Super Eagles ta doke kungiyar Pharaohs ta Masar

Hotunan yadda Najeriya ta doke Masar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, 'Yan wasan Najeriya suna murna bayan yin nasara a rukunin Group D na Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka a wasansu da 'yan wasan Masar a filin wasa na Stade Roumde Adjia da ke Garoua
An wallafa

Najeriya ta doke Masar da ci 1-0 a rukunin D na gasar cin kofin Nahiyar Afirka ta 2021.

Dan wasan Najeriya wanda ke buga wasa a Leicester City Kelechi Iheanacho ne ya zura kwallon a minti 30 da soma wasa.

Wasan shi ne mafi zafi kawo yanzu saboda girman ƙasashen a tarihin gasar cin kofin Afirka

An yi fafatawar ne a birnin Garoua na Kamaru da misalin ƙarfe huɗu na yamma agogon Najeriya da Kamaru.

Ga hotunan yadda Super Eagles ta doke Pharaohs ta Masar

Hotunan yadda Najeriya ta doke Masar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wannan shi ne karo na tara da aka kece raini tsakanin Najeria da Masar a gasar cin kofin nahiyar Afirka.
Hotunan yadda Najeriya ta doke Masar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, 'Yan wasan Najeriya sun taka rawar gani sosai a wannan fafatawar. Sai dai kafin wannan karawar, Najeriya ta yi nasara a kan Masar sau uku da canjaras uku, amma a wasan karshe da suka hadu a 2010, Masar ce ta doke Super Eagles da ci 3-1.
Mohamed Salah

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shahararren dan wasan Liverpool Mohamed Salah ya gaza yin katabus a wasan na yau
Hotunan yadda Najeriya ta doke Masar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wannan shi ne karo na 19 da Super Eagles take buga Afcon, wadda take kai wa daf da karshe a wasa 14 daga 16 da ta halarta, wadda ta lashe kofin karo uku jumulla.
Hotunan yadda Najeriya ta doke Masar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Magoya bayan Najeriya sun yi ta murna bayan da kasarsu ta yi nasara a wasan