Best Fifa Awards: Salah da Messi da Lewandowski na takarar gwarzon dan kwallon kafar Fifa

An wallafa

Dan wasan Liverpool Mohamed Salah da dan kwallon Paris St-Germain Lionel Messi da kuma dan wasan Bayern Munich Robert Lewandowski na ciki jerin 'yan wasan da ke takarar zama gwarzon dan kwallon kafar Fifa na bana a rukunin maza.

A bangaren mata, 'yar wasan Chelsea Sam Kerr da 'yan wasan Barcelona Jennifer Hermoso da Alexia Putellas na cikin wadanda ke fatan zama gwarzuwar 'yar kwallon Fifa.

Za a sanar da gwarzo da gwarzuwar Fifa, wadda ake yi wa lakabi da Best Fifa Football Awards, a birnin Zurich ranar 17 ga watan Janairu.

Kociyoyi na manyan kungiyoyin kwallon kafar duniya da kyaftin-kyaftin na manyan kulob-kulob da 'yan jarida da kuma masu sha'awar kwallon kafa ne suke zaben gwarazan 'yan kwallon kafar Fifa.

A halin yanzu dan kasar Masar, Salah shi ne dan wasan da ya fi zura kwallo a raga a Premier League, inda ya ci 6.

Ita kuwa 'yar kasar Australia, Kerr ta taimaka wa Chelsea kare kambunta na Women's Super League na 2021 sannan ta kai zagayen karshe a gasar Zakarun Turai na Champions League.

Lewandowski ne ya lashe gasar gwarzon dan kwallon Fifa na 2020, yayin da 'yar wasan Manchester City Lucy Bronze ta yi nasara a bangren mata.