Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lewandowski ne kan gaba a cin kwallaye a Turai a 2020/21
Robert Lewandowski ya lashe takalmin zinare a matakin wanda ke kan gaba a yawan cin kwallaye a nahiyar Turai a kakar 2020/21
Dan kwallon tawagar Poland ya ci kwallo 41 a kakar Bundesliga da ta wuce, wanda ya zama na biyu da ke taka kwallo a Jamus daga waje da ya karbi kyautar bayan bajintar da Gerd Muller ya yi a 1970 da kuma a 1972.
Haka kuma Lewandowsi ya kawo karshen tarihin zura kwallo a raga da Gerd Muller ya kafa na cin kwallo 40 tun bayan shekara 50.
Kyaftin din tawagar Argentina, Lionel Messi mai wasa yanzu haka a Paris St Germain, shine na biyu da ya ci kwallo 30 a La Liga tare da Barcelona a 2020/21.
Wanda ya yi na uku shine kyaftin din Portugal, Cristiano Ronaldo, wanda ke buga wa Manchester United tamaula, wanda ya zura kwallo 29 a gasar Serie A tare da Juventus a kakar da ta wuce.
Lewandowski ya karbi kyautar takalmin zinare daga hannun Ciro Inmobile, wanda ya zama zakara a kakar 2019/20 a bikin da rukunin European Sports Media ke gabatarwa tun daga 1968, in banda 1990 da aka ci karo da cikas.
Kamar yadda aka tsara fitar da zakara, duk dan wasan da ya ci kwallo a daya daga manyan gasar Turai biyar, yana da maki biyu, yayin da kasa da gasar ka samu maki 1.5 da wadanda ake bai wa maki daya, ya dai danganta da darajar gasar da kake buga wa a nahiyar Turai.
Bayan Muller an samu fitattun 'yan wasan tamaula da suka ci kyautar da suka hada da Lionel Messi da Cristiano Ronaldo da Francesco Totti da Thierry Henry da Ronaldo da Marco van Basten da Hristo Stoichkov da kuma Eusebio.
Wasu tsoffin yan kwallon Bayern Munich da suka lashe kyautar sun hada da Roy Makaay a lokacin da yake wasa a Deportivo La Coruna da kuma uca Toni lokacin da yake taka leda a Fiorentina.