Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ferran Torres: Barcelona ta tabbatar da daukar dan wasan Manchester City
Ferran Torres ya koma taka leda a Barcelona daga Manchester City kan yarjejeniyar da za ta kare a karshen Yunin 2027.
Tuni dai Barcelona ta gindaya kudi Yuro biliyan daya, kwatankwacin fam miliyan 842 ga duk wadda ke son daukar dan wasan Sifaniya, idan kwantiraginsa bai kare a Camp Nou ba.
Mai shekara 21 ya sake komawa Sifaniya da taka leda, bayan wata 18 da ya bar Valencia ya koma City da buga tamaula.
Kungiyoyin biyu ba su fayyace kudin cinikin dan kwallon ba, amma dai ana rade radin cewar zai kai fam miliyan 46.3.
Cikin Oktoba Ansu Fati da Pedri suka sabunta kwantiraginsu a Barcelona, mai dauke da Yuro biliyan daya kowanne ga duk mai san daukarsu, idan yarjejeniyarsu ba ta kare a kungiyar ba.
Kocin City, Pep Guardiola ne ya sanar da batun Torres zai koma Barcelona a makon jiya, har ma ya taya shi murna.
An fahimci cewar Barcelona za ta biya karin fam miliyan 8.4 kudin tsarabe-tsarabe, kuma kungiyar Camp Nou za ta sayar da wasu 'yan wasan, domin cika ka'idar kashe kudi daidai samu a dokar La Liga.
Torres dan kwallon tawagar Sifaniya ya buga wasa 43 da cin kwallo 16 a City tun daga Agustan 2020 da ya koma Etihad daga Valencia.
Ya yi wa City wasa shida a kakar bana daga nan aka ajiye shi a benci, bai kara yi wa kungiyar wasa ba, tun bayan da ya ji rauni a lokacin da ya yi wa Sifaniya tamaula a cikin watan Oktoba.
Torres ne da kansa ya bukaci izinin barin City, domin ya gwada sa'a a wata kungiyar, inda Guardiola ya amince da hakan, bayan da yake da Bernardo Silva da Jack Grealish da Riyad Mahrez da Raheem Sterling da Gabriel Jesus da kuma Phil Foden da kowanne ke kan ganiya.
Barcelona na fama da rashin mai cin kwallaye a kakar nan da fama da matsin tattalin arziki da ta kai Lionel Messi ya bar kungiyar zuwa Paris St Germain a farkon kakar nan - sannan Antoine Griezmann ya sake komawa Atletico Madrid.
A kakar nan Sergio Aguero ya koma Barcelona daga Manchester City, bayan da yarjejeniyarsa ya kare a Etihad, sai dai kuma mai shekara 33 ya yi ritaya sakamakon matsalar bugun zuciya da yake kasa nunfashi yadda ya kamata.