Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasuwar ƴan kwallo: Makomar Sancho, Haaland, Rice, Kane, Goretzka da Torres
Manchester City za ta yi zama da dan kwallon tawagar Ingila, Raheem Sterling kan fayyace makomarsa, bayan da saura kaka biyu za ta kare a kungiyar wadda ta lashe Premier League. (Mail)
Bayan da Borussia Dortmund ta sayar da Jadon Sancho, Manchester United tana da sauran 'yan wasan da take fatan dauka daga cikin dan kwallon West Ham, Declan Rice, mai shekara 22, da dan wasan Villarreal mai shekara 24 mai tsaron baya Pau Torres da na Tottenham, Harry Kane, mai shekara 27. (Guardian)
Za a bai wa Sancho riga mai lamba bakwai a Manchester United, wadda a yanzu dan wasan tawagar Uruguay, Edinson Cavani, mai shekara 34 ke sanyawa. (Metro)
United na son daukar dan wasan Bayern Munich mai buga wa tawagar Jamus tamaula, Leon Goretzka, mai shekara 26, wanda yarjejeniyarsa da kungiyar da ke buga Bundesliga za ta kare a karshen kakar 2022. (Bild - in German)
Watakila Manchester United da Liverpool su hakura da batun rigen daukar dan wasan tawagar Faransa Kingsley Coman bayan da Bayern ta yi masa farashin fam miliyan 77, kudin dan wasan mai shekara 25. (Bild)
Shugaban Paris St-Germain, Nasser Al-Khelaifi ya karbi aikin matsayin daraktan wasannin kungiyar da Leonardo ke yi don tattaunawa da dan kwallon tawagar Faransa, Kylian Mbappe don tsawaita zamansa a kungiyar. Kwantiragin dan kwallon mai shekara 22 za ta kare a karshen kakar 2022. (L'Equipe, via Get French Football News)
Mai kungiyar Chelsea, Roman Abramovich yana da tabbacin zai dauko dan kwallon Borussia Dortmund, Erling Braut Haaland, mai shekara 20 zuwa Stamford Bridge a bana. (Express)
Likitoci a Arsenal za su auna koshin lafiyar matashin dan wasan tawagar Portugal mai shekara 21, Nuno Tavares, don komawa Gunners kan fam miliyan bakwai daga Benfica. (Goal)
Chelsea ta yi wa dan wasan Manchester United, Lauren James, mai shekara 19 ta yin karshe. (Goal)
Leicester na fuskantar kalubale daga AC Milan kan shirin sayen dan wasan Sassuolo, Domenico Berardi, mai shekara 26, wanda ya burge Milan a gasar cin kofin nahiyar Turai ta Euro 2020 da yake wakiltar tawagar Italiya. (Corriere dello Sport - in Italian)