Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Gomez, Coman, Martial, Azpilicueta, Marquinhos, Milinkovic-Savic

An wallafa

Real Madrid na sa ido kan dan wasan baya na Liverpool da Ingila, Joe Gomez mai shekara 24. (Mail)

Manchester United, Barcelona da Real Madrid duka na sha'awar sayo dan wasan Faransa da Bayern Munich, Kingsley Coman mai shekara 25. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Liverpool na cikin kungiyoyi masu son raba Erling Braut Haaland da Borussia Dortmund dan wasan gaba dan asalin Norway mai shekara 21. (Sky Germany)

Anthony Martial, dan wasan gaba mai shekara 26 na kungiyar Manchester United da Faransa yafi son zuwa Sevilla a matsayin dan aro. (Sky Sports)

Cesar Azpilicueta, wanda shi ne kyaftin din Chelsea kuma dan wasa mai shekara 32 ya fi son ci gaba da taka leda a kungiyar duk da sha'awar da Barcelona ke nunawa kan daukar dan kasar Sfaniyar. (The Athletic - subscription required)

Manchester United ta tuntubi River Plate kan kulla yarjejeniyar daukan Julian Alvarez, dan wasan gaba dan Argentina mai shekara 21 kan fam miliyan 17. (Ole - in Spanish)

Manchester United na sha'awar daukar Sergei Milinkovic-Savic, dan wasan tsakiya kuma dan Serbia daga Lazio. (Il Messaggero - in Italian)

Paris St-Germainta ki amincewa da tayin da Chelsea ta yi ma ta kan dan wasanta na bayaMarquinhos mai shekara 27 kan fam miliyan 72. (L'Equipe - in French)

Marquinhos dan asalin kasar Brazil zai tsawaita kwantiraginsa da PSG zuwa 2026 ko 2027. (Fabrizio Romano)