Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man Utd ta bude sansaninta na atisaye da ke Carrington bayan bullar cutar korona
Manchester United ta bude sansanin horonta da ke Carrington, bayan da ta rufe shi, bayan da cutar korona ta bulla a can.
United ta fara rufe wasu wurare a Carrington a makon jiya, sannan aka dage mata wasan Premier League da ya kamata ta buga da Brentford da kuma Brighton.
Ranar Litinin kungiyoyin Premier League da mahukuntan gasar suka cimma matsayar ci gaba da wasannin kakar bana, duk da kalubalen da suke fuskanta daga annobar.
United ta sanar cewar bude sansanin zai bai wa koci, Ralf Rangnick da 'yan wasa su ci gaba da shirye-shiryen tunkarar zuwa Newcastle United a St James Park ranar Litinin 27 ga watan Disamba, don buga wasan Premier.
United ta samu 'yan wasa da jami'anta da suka kamu da cutar, bayan karawa da Norwich City da ta yi nasara da ci 1-0 ranar 11 ga watan Disamba, bayan da ta gudanar da gwaji kwana daya tsakani.
A karshen mako aka dage wasa shida a Premier League don gudun yada annobar, kuma a makon nan mahukuntan gasar suka sanar cewar sabbin mutun 90 sun kamu da annobar daga gwajin 'yan wasa da jami'ai 12,345 da ta yi tsakanin 13 zuwa 19 ga watan Disamba.