'Yan wasan Arsenal na fama da ciwon ciki

Arsenal

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Kocin Arsenal Mikel Arteta ya tabbatar da cewa akwai yan wasansa da rashin lafiya za ta hana su zuwa Leicester, a wasan Premier na ranar Asabar.

Mai tsaron baya Pablo Mari dama bai buga wasan kofin Carabao ba da suka yi nasara a gida da Leeds United, yayin da aka cire Ben White ana tsakiyar wasa.

"Rashin lafiya ce dai haka ta kama wasu yan wasa musamman ciwon ciki, amma dai muna fatan kowa zai warke," in ji Arteta.

Ya kara da cewa "akwai ma wadanda basu samu yin atisaye ba amma dai muna fatan samun labari mai dadi game da halin da suke ciki."

"Har kawo yanzu White bai yi atisaye ba, saboda haka ba za mu iya yanke hukuncin ko zai buga wasa gobe ba ko kuma a'a,"in ji Arteta.

Gunners sun buga wasa shida a Premier League ba a doke su ba, kuma suna zaune na 10 a teburi maki uku tsakaninsu da hudun farko.