An ci tarar Chelsea fam 25,000, bayan 'yan wasa sun kalubalanci jan katin Reece

Chelsea players surround referee Anthony Taylor

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Lokacin da 'yan wasan Chelsea ke kalubalantar alkalin wasa, Anthony Taylor kan jan kati da ya yi wa Reece James
An wallafa

Chelsea za ta biya tarar fam 25,000, bayan da ta kasa tsawatarwa 'yan wasanta, lokacin da aka bai wa Reece James jan kati a karawa da Liverpool cikin watan Agusta.

Alkalin wasa Anthony Taylor ya kori James daga karawar, wanda ya sawa kwallo hannu a kan layin raga, daga baya aka bayar da fenaritin da Mohammed Salah ya buga ya farke kwallon da Chelsea ta zura a gasar Premier League.

'Yan wasan Chelsea sun harzuka da hukuncin Taylor, inda suke cewa kwallon ya fara bugar cinyar dan wasan tawagar Ingila kafin ya taba hannun sa.

Hukuncin da aka yanke shine James ba zai buga wa Chelsea gasar Premier League da za ta fafata da Aston Villa ranar Asabar a Stamford Bridge ba.

''An ci tarar Chelsea fam 25,000 bayan karya dokar hukumar kwallon kafar Ingila biyu a lokacin gasar Premier League da Liverpool ranar Asabar 28 ga watan Agustan 2021,'' in ji jawabin hukumar.

''Ta kara da cewar kungiyar ta kasa tsawatarwa 'yan wasanta kan halayyar tada yamutsi da suka yi kan hutu da kuma a zagaye na biyu a fafatawar.''

Bayan da kungiyoyin suka tashi 1-1, kowacce ta buga karawa uku da fara gasar Premier League ta bana ba tare da yin rashin nasara ba.