Manchester United: Jesse Lingard bai yadda ya tsawaita zam,ansa a Old Trafford ba

An wallafa

Dan kwallon Ingila, Jesse Lingard ya yi watsin tsawaita yarjejeniyar sa da Manchester United ta gabatar masa.

An fahimce cewar Lingard na tunanin da kyar ne idan za a dunga saka shi a wasannin United, musamman da Cristiano Ronaldo ya koma kungiyar a bana.

Lingard, wanda ya ci wa Ingila kwallo biyu a karawa da Andorra ranar Lahadi a wasan neman shiga gasar kofin duniya, ya taka rawar gani a wasannin aro da ya buga a West Ham a kakar da ta wuce.

Kwantiragin dan wasan mai shekara 28, zai kare a karshen kakar bana a Manchester United.

West Ham United ta taya Lingard a lokacin da aka yi cinikayyar 'yan kwallo, domin ta mallaki dan wasan, amma United ba ta sallama shi ba.

Dan kwallon ya buga wa United minti hudu a bana a wasan Premier League da Southampton da suka tashi 1-1 a watan jiya.

Har yanzu United ba ta fayyace yadda za ta dunga saka shi a wasanni ba, bayan da Ole Gunnar Solskjaer ke fuskantar karawar Champions League da Carabao Cup da kuma gasar Premier League.