An dage wasan Barca da Sevilla da na Villareal da Alaves

An wallafa

Hukumar wasanni ta Sifaniya ta dakatar da karawa tsakanin Barcelona da Sevilla da na Villareal da Alaves da ya kamata su buga ranar Asabar.

Hukumar kwallon kafa ta Sifaniya ce ta shigar da korafin cewar ya kamata a dake fafatawar da ya kamata kungiyoyin su yi a gasar La Liga a karshen makon nan.

Hakan ya biyo bayan da hukumar kwallon kafa ta duniya, Fita ta kara kwanakin buga wasannin neman gurbin shiga gasar kofin duniya a shiyyar Kudancin Amurka.

Fifa ta yi hakan ne don bai wa tawagogin Kudancin Amurka damar buga kwantan wasan da cutar korona ta sa ba a buga ba.

Wannan hukuncin na nufin 'yan wasan da ke taka leda a Sifaniya ba za su koma kungiyoyin su ba har sai zuwa ranar Juma'a da yammaci, kwana daya a buga wasannin La Liga karawar mako na hudu.

Da yake Barcelona da Villareal za su buga gasar Champions League ranar Talata, mahukuntan La Liga sai suka bukaci kungiyoyin da su yi wasan su ranar Asabar.

Hakan ne ya sa hukumar kwallon kafa ta Sifaniya ba ta amince da hukuncin masu gudanar da La Ligar ba, har suka kai kara ga hukumar wasannin kasar, wadda ta dakatar da fafatawar kungiyoyin a ranar Asabar a gasar La Liga.