Cristiano Ronaldo: Manchester United ta bai wa kyftin din Portugal lamba 7

An wallafa

Manchester United ta sanar cewar Cristiano Ronaldo zai saka mata riga mai lamba 7 a kungiyar.

Mai shekara 36 ya karbi lambar da ya yi amfani da ita a zaman sa na farko a Old Trafford daga Edison Cavani - yanzu ya karbi lamba 21.

Ronaldo zai fara atisaye a Manchester United da zarar ya kammala killace kan sa na kwana biyar.

Ranar Alhamis tawagar Portugal ta bai wa dan kwallon damar barin sansanin da take, bayan da aka yi masa jan kari, sakamakon cire riga a wasa da Ireland ranar Laraba.

United ta rubuta a shafinta na Inter cewar ''Zakakurin dan kwallon Portugal ya saka riga mai lamba 7 a zaman farko da ya yi a Old Trafford, zai ci gaba da amfani da ita da zarar ya isa kungiyar''.

Ronaldo ya kammala komawa Old Trafford ranar Talata, zai kuma yi wa Manchester United wasan farko a karo na biyu a fafatawar Premier League da Newcastle United ranar Asabar 11 ga watan Satumba.

Ronaldo ya zama kan gaba a tarihin ci wa tawaga kwallaye a duniya, bayan da ya zura biyu a ragar Ireland, amma an yi masa jan kati sakamakon cire riga da ya yi a lokacin murna.

Kawo yanzu Ronaldo ya zura 111 a raga a tawagar Portugal, ya kuma dara Ali Daei na Iran mai bajintar cin 109 tsakanin 1993 zuwa 2009.