Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Cristiano Ronaldo ya zama kan gaba a yawan ci wa tawaga kwallaye a duniya
Cristiano Ronaldo ya zama kan gaba a yawan ci wa tawaga kwallaye a duniya, bayan da Portugal ta doke Ireland da ci 2-1 ranar Laraba.
Portugal ta karbi bakuncin Ireland a wasan neman shiga gasar cin kofin duniya da Qatar za ta karbi bakunci a 2022.
Minti 15 da fara tamaula, Portugal ta samu bugun daga kai sai mai tsaronraga, inda kyaftin Ronaldo ya buga amma ya barar.
Daf da su je hutu ne Ireland ta ci kwallo ta hannun John Egan haka suka ci gaba da fafatawar, duk da hare-haren da Portugal ke ta kai wa.
A minti na 89 ne Ronaldo ya farke, sannan ya kara na biyu kasa da minti daya tsakanin ta farko da ya zura a raga.
Dan kwallon Manchester United ya kafa tarihin ci wa Portugal kwallo 111 kenan jumulla, shine kan gaba a duniya a wannan bajintar.
Wanda ya kafa tarihin ci wa Iran kwallaye shine Ali Daei mai 109 a raga, yanzu Ronaldo ne kan gaba.
Ronaldo ya yi wannan namijin kokarin da ya ci kwallo 49 a karawa 47 baya da ya yi wa kasar.
Da wannan sakamakon Portugal ce ta daya a rukunin farko da maki 10, bayan wasa hudu da tazarar maki uku tsakaninta da Serbia.