Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Marcel Sabitzer: Kyaftin din RB Leipzig ya koma Bayern Munich
Bayern Munich ta kammala daukar kyaftin din RB Leipzig, Marcel Sabitzer kan yarjejeniyar kaka hudu.
Dan kwallon Austria, mai shekara 27, wanda zai sa riga mai lamba 18 ya yi kaka bakwai a Leipzig, wanda ya zama kashin bayan kungiyar tun bayan da ta samu gurbin buga Bundesliga a 2016.
Sabitzer, wanda ya yi wa Leipzig wasa 229 zai taka leda karkashin kocin da ya horar da shi a baya Julian Nagelsmann da wanda suka taka leda a tare mai tsaron baya Dayot Upamecano, wanda ya koma Bayern daga Red Bull Arena a bana.
Nagelsmann da Sabitzer da kuma Upamecano sun taimakawa Leipzig ta yi ta biyu a gasar Bundesliga a bara da Bayern ta lashe da kai wa wasan karshe a German Cup, wanda Borussia Dortmund ta dauka bayan tashi wasa 4-1.
Bayern ta fara kakar bana da kafar dama karkashin Nagelsmann, mai shekara 34, wan ya hada maki bakwai a wasa uku a gasar Bundesliga ta bana.
Ya kuma ja ragamar kungiyar da ta doke Borussia Dortmund ta ci gaba da rike German Super Cup a kakar nan.
Haka kuma Bayern ta doke Bremen SV 12-0 karkashin Nagelsmann a German Cup, wasan farko da ta dura kwallaye da yawa a raga tun bayan 1977.
Bayan koci Nagelsmann da Upamecano da Sabitzer da suka koma Bayern a bana ta kuma dauki Omar Richards da kuma Sven Ulreich - wanda ya buga wa kungiyar wasanni tsakanin 2015 da kuma 2020 - daga nan ya koma Reading sannan ya je Hamburg.