Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Edinson Cavani: Uruguay ta soke gayyatar dan wasa Manchester United
Edinson Cavani zai ci gaba da zama a Manchester United a lokacin da ake wasannin shiga gasar kofin duniya, bayan da Uruguay ta soke goron gayyatar da ta yi masa.
Kungiyoyin Premier League ne suka ce ba za su bar 'yan wasa su buga wa kasashen su wasanni ba, wadanda suka ayyana wurin da ake da hadarin kamuwa da cutar korona.
Tun farko Cavani ba zai yi wa United wasanni ba,, bayan da hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa ta kara kwana biyu a kalandar Kudancin Amurka.
Kuma yadda doka ta tanada a Birtaniya, idan ya koma Ingila sai ya killace kansa kwana 10, kafin ya koma taka leda.
Cavani ba zai samu damar buga wa Uruguay wasan neman shiga gasar cin kofin duniya da za ta yi da Peru da Bolivia da kuma Ecuador ba.
Lamarin 'yan wasan Kudancin Amurka da ke taka leda a Sifaniya ya sa mahukuntan La Liga sun bukaci hukumar kwallon kafar kasar da ta soke karawa ta ranar 11 ga watan Satumba tsakanin Villarreal da Alves da na Sevilla da Barcelona.
Sai dai 'yan wasan Tottenham, Giovani Lo Celso da kuma Cristian Romero za su je buga wa Argentina wasanni - daya daga kasashen da aka sa cikin masu hadarin kamuwa da cutar korona - hakan na nufin ba za su yi wa Tottenham wasa uku ba idan sun koma Ingila.
Argentina za ta buga wasan neman gurbin shiga gasar kofin duniya da Venezuela da Brazil da kuma Bolivia - saboda haka mai buga gasar Premier sai ya killace kansa a otal din gwamnati na kwana 10 idan ya koma kasar.