Man United ta kafa tarihin yawan wasa a Premier a waje ba a doke ta ba

An wallafa

Ranar Lahadi Manchester United ta je Molineux ta doke Wolverhampton da ci 1-0 a wasan mako na uku da fara kakar Premier League.

Mason Greenwood ne ya ci wa United kwallon da ta hada maki ukun da take bukata a fafatawar.

Da wannan sakamakon United ta kafa tarihin yawan buga wasanni a waje a babbar gasar Ingila ba tare da an doke ta ba ranar Lahadi.

Kungiyar ta Old Trafford ta yi wasa 28 a waje kenan ba tare da yin rashin nasara ba, wadda ke rike da tarihin ita ce Arsenal mai wasa 27 a kakar 2003/04.

United ta yi wasa na 27 a waje ba a doke ta ba a makon jiya da ta tashi 1-1 a gidan Southampton a karkashin jagorancin Ole Gunnar Solkjaer.

Wasan karshe da aka doke United a Premier League shine wanda Liverpool ta yi nasara a Anfield ranar 19 ga watan Janairun 2020.

Tun daga lokacin zuwa yanzu United ta ci fafatawa 18 da canjaras 10 a wasannin waje da ta yi ba tare da an doke ta ba.

Kuma cikin wannan bajintar United ta ci kwallo 50 a raga aka zura mata 18, kuma Bruno Fernandes ne kan gaba da kwallo 15 cikin wasannin wajen da ta yi tarihin.

Wasan na ranar Lahadi shine na 100 da Solskjaer ya ja ragamar United a Premier League, kuma koci na tara da ya yi wannan namjin kokarin a Old Trafford.