Robert Lewandowski: Ya ci wa Bayern Munich kwallo a wasa 16 a jere

Robert Lewandowski

Asalin hoton, Bayern Munich FC

An wallafa

Bayern Munich ta yi nasarar doke Hertha Berlin da ci 5-0 a wasan mako na uku a gasar Bundesliga da suka fafata ranar Asabar.

Thomas Mueller ne ya fara cin kwallo minti uku da fara tamaula, sai Robert Lewandowski ya ci na biyu saura minti 10 su je hutu.

Minti hudu da komawa zagaye na biyu ne Jamal Musiala ya ci na uku, sai Robert Lewandowski ya kara na hudu, sannan saura minti shida a tashi daga gumurzun Lewandowski ya ci na uku.

Da wannan sakamakon Lewandowski ya ci kwallo a kowanne wasa 16 a jere da ya yi wa Bayern Munich a kowacce fafatawa kenan.

Mai shekara 33 ya fara kafa wannan bajintar tun wasan da Bayern ta tashi 3-3 da Arminia Bielefeld ranar 15 ga watan Fabrairu.

Haka kuma kwallon farko da Lewandowski ya zura a raga ta zama na 299 da ya ci wa Bayern Munich da na 300 da kuma na 301 a kungiyar.

Tsohon dan kwallon tawagar Jamus, Gerd Mullar, wanda ya mutu ranar 15 ga watan Agusta, ya ci kwallo a kowanne wasa 15 a jere da ya yi bajintar a Bayern Munich a 1969-70.