Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ansu Fati ya koma atisaye bayan jinyar wata tara
Matashin dan wasan Barcelona, Ansu Fati ya koma atisaye a karon farko ranar Talata, tun bayan jinyar wata tara.
Barcelona ta fada cewar dan kwallon mai shekara 18 ya yi atisaye cikin 'yan wasa a safiyar Talata, yayin da jaridar Marca ta ce watakila Fati ya buga wa Barcelona wasan da za ta yi da Sevilla ranar 11 ga watan Satumba a gasar La Liga.
Fati ya ci kwallo hudu a karawa La Liga shida a bara, daga nan ya ji rauni a karawar da Barcelona ta doke Real Betis da ci 5-2 cikin Nuwambar 2020.
Tun farko likitoci sun yi masa aiki a gwiwar kafar sa, wanda ya yi kwana biyar a asibiti daga baya aka sallameshi, inda Barcelona ta ce zai yi jinyar mako hudu.
Daga baya aka sake yi masa aiki a kafar a watan Yuni a Porto, bayan da raunin bai warke ba kamar yadda aka sa rai tun farko.
Fati ya zama matashin Barcelona na farko da ya ci kwallo a La Liga a fafatawa da Osasuna cikin Agustan 2019.
Kaka daya tsakani ya zama matashin dan wasan Sifaniya da ya zura kwallo a raga a wasan da Sifaniya ta doke Ukraine 4-0 a UEFA Nations League a cikin Satumbar 2020.
Idan Fati ya koma buga wa Barcelona tamaula zai kara karfin kungiyar, wadda ke fuskantar matsin tattalin arziki a bana, kuma Lionel Messi ya koma Paris St Germain a bana, wayan shekara 21 a Camp Nou.