Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Aubameyang, Kane, Saul, Rice, Kounde, Camavinga, Nketiah, Moore

An wallafa

Arsenal za ta saurari duk wani tayi da za a yi wa kyaftin dinta Pierre-Emerick Aubameyang, mai shekara 32, kuma ta ce ba za ta hana dan Gabon din tafiya ba idan yana so ya bar kungiyar kafin lokacin rufe kasuwar sayar da 'yan kwallo ta yanzu ba. (Jaridar Telegraph)

Kungiyar ta Gunners ta kuduri aniyar tallafa wa kociyanta Mikel Arteta wanda ke cikin matsi sakamakon doke su da aka yi a wasanninsu biyu na farkon bude gasar Premier. (Jaridar Mirror)

Shugaban Tottenham Daniel Levy ba zai rage farashin da ya yi wa Harry Kane ba, kuma zai iya kin sallama kyaftin din na Ingila mai shekara 28 a farashin fam miliyan 150, wanda shi ne mafi tsada a cinikin dan wasa a Birtaniya, daga Manchester City. (Jaridar Telegraph)

Chelsea na duba yuwuwar karbar aron dan wasan tsakiya na Atletico Madrid da Sifaniya Saul Niguez, mai shekara 26, yayin da kungiyar ta Blues ta ba wa 'yan bayanta Antonio Rudiger, mai shekara 28, na Jamus da dan Denmark Andreas Christensen, mai shekara 25 sabon kwantiragi. (Telegraph)

Dan wasan tsakiya dan Ingila Declan Rice ya shirya yi watsi da duk wani sabon kwantiragi daga West Ham, saboda dan wasan mai shekara 22 yana ganin kungiyar ta tsauwala masa farashi don kada a samu mai sayensa a bazaran nan. Yana da sauran shekara uku da ta rage a kwantiraginsa na yanzu kuma kungiyar tana da damar kara masa shekara daya. (Jaridar Times)

Chelsea na da fatan sayen dan bayan Faransa Jules Kounde daga Sevilla, dan wasan mai shekara 22 da aka ce yana da farashin fam miliyan 77 na na-gani-ina-so a kwantiraginsa. Kungiyoyin biyu sun so a ce cinikin ya hada da dan bayan Chelsea Kurt Zouma, mai shekara 26, amma kuma sai Zouman ya ki yarda ya je kungiyar ta La Liga. (90Min)

Har yanzu Manchester United tana son sayen dan wasan tsakiya na Rennes Eduardo Camavinga, mai shekara 18, amma kuma tana ganin dan wasan na Faransa zai fi son ya tafi Paris St-Germain ko wata kungiya ta Sifaniya. (ESPN)

West Ham na duba yuwuwar daukar dan wasan tsakiya na Lille dan Faransa Jonathan Bamba, mai shekara 25, a madadin Jesse Lingard dan Ingila, daga Manchester United. (Jaridar Express)

Crystal Palace a shirye take ta biya fam miliyan 10 a kan dan wasan gaba na Arsenal Eddie Nketiah, mai shekara 22, amma kuma Gunners din sun kafe a farashin da kusa fam miliyan 20. Dan wasan wanda ya fi kowa cin kwallo a tarihi a tawagar Ingila ta 'yan kasa da shekara 21 ya samu tayi ma daga Jamus a bazaran nan. (Athletic)

Dan wasan tsakiya na Arsenal Lucas Torreira, 25, mai shekara na dab da tafiya Fiorentina aro. Daman dan wasan na tsakiya dan Uruguay ya yi kakar da ta gabata ne a Atletico Madrid, inda ya taimaka wa kungiyar ta Diego Simeone cin La Liga. (football.london)

Dan wasan tsakiya na Brazil Willian, mai shekara 33, na shirin barin Arsenal ba tare da wani kwantiragi a kansa ba, domin tafiya Corinthians ta kasarsa, kuma tuni tattaunawa ta yi nisa a kan hakan. (Jaridar Mail)

Wolves na shirin tayin fam miliyan 7 a kan dan wasan gaba na Cardiff City da Wales Kieffer Moore, mai shekara 29. (Football Insider)

Dan bayan Manchester United Phil Jones a shirye yake ya duba yuwuwar tafiya wata kungiya ta kasa gasar Championship, wato kasa da Premier, saboda kimar dan wasan na baya mai shekara 29 ta ragu a Old Trafford. (Football League World)

Ga alama Newcastle United da West Ham za su yi gogayya da Burnley wajen sayen dan bayan Ivory Coast Maxwel Cornet, mai shekara 24, daga Lyon. (90 Min)

Sheffield United ta yi watsi da tayin da Everton ta yi a kan dan wasan gaba Daniel Jebbison mai shekara 18, haifaffen Canada, wanda ya taka wa Ingila wasa a gasar matasa. Aston Villa da Brentford da ma Leeds na sha'awar matashin dan wasan. (Teamtalk)