Andy Robertson: Dan kwallon Scotland zai ci gaba da taka leda a Liverpool zuwa 2026

Liverpool left-back Andy Robertson

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Robertson bai buga wa Liverpool wasa biyu da ta yi ba a kakar bana ta Premier League
An wallafa

Mai tsaron bayan Liverpool, Andy Robertson ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da taka leda a kungiyar zuwa karshen kakar 2026.

Mai shekara 27, kyaftin din tawagar Scotland ya koma Anfield da taka leda a Yulin 2017 daga Hull City kan fam miliyan takwas, kawo yanzu ya yi wasa 177 a kungiyar.

Robertson ya bi sahun wasu 'yan wasan Liverpool da suka tsawaita kwantiragin zama a Anfield a bana da suka hada da Trent Alexander-Arnold da Fabinho da Alisson da kuma Virgil van Dijk.

Robertson ya lashe Premier League da Champions League da Fifa Club World Cup da kuma Uefa Super Cup a Liverpool.

Dan kwallon ya ji rauni a lokacin atisayen tunkarar kakar bana a wasan sada zumunta da Athletic Bilbao da hakan ya hana shi buga wasa a kakar bana.

Saboda haka dan kwallon tawagar Scotland bai buga wa Liverpool wasan Premier biyu ba, wanda ta yi nasara a kan Norwich City da kuma Burnley.

Robertson ya ce raunin da ya ji ba wani mai girma bane, yana kuma cikin 'yan wasan Scotland da za su buga mata wasan neman gurbin shiga gasar kofin duniya a watan Satumba.