Virgil van Dijk: Dan kwallon Liverpool zai ci gaba har zuwa 2025

Virgil van Dijk

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Virgil van Dijk ya zama katanga a bayan Liverpool
An wallafa

Dan kwallon baya na Liverpool, Virgil van Dijk ya tsawaita kwantaraginsa a kulob din har zuwa shekara ta 2025.

Dan wasan mai shekara 30, ya bi sawun Trent Alexander-Arnold, Fabinho da kuma Alisson wajen tsawaita zamansu a kungiyar.

Saboda fama da rauni, sau biyar kacal ya murza a kakar wasan da ta wuce.

Van Dijk wanda ya soma atisaye a 'yan makonnin da suka wuce, ya bayyana cewa "na ji dadin wannan matakin na sabunta kwagilata".

Tun lokacin da Van Dijk ya koma Liverpool a watan Janairun 2018, kungiyar ta lashe wasanni 72 daga 95 a gasar firemiya.