Kasuwar ƴan kwallo: Makomar Lukaku, Ramsdale, Varane, Abraham, Kounde, Vestergaard, Martial

Asalin hoton, Getty Images
Romelu Lukaku na dab da kammala komawa tsohuwar kungiyarsa wato Chelsea, bayan da kungiyarsa Inter Milan ta aminta da tayin fam miliyan 97.5. (Sky Sports)
Wata majiya ta ce tuni dan wasan mai shekaru 28 ya isa birnin London daga Milan.
Manchester United na dab da sanar da sayen mai tsaron bayan Faransa Raphael Varane daga Real Madrid a yau Alhamis. (Sun)
Ita kuma Chelsea ta aminta da tayin fam miliyan 34 da Roma ta yi mata kan dan wasan gabanta Tammy Abraham mai shekaru 23. (Goal)
To amma akwai rahotannin da ke cewa itama Arsenal ta ce za ta taya dan wasan matsawar ta saida Alexander Lacazatte zuwa Roma.
A London kuwa Arsenal na ci gaba da tattauwana da Sheffield United don ganin ta sayi mai tsaron gidanta Aasron Ramsdale akan fam miliyan 24 zuwa fam miliyan 30. (Football. London)
A Sifaniya Sevilla ta ce a shirye take ta sayar wa da Chelsea Jules Kounde mai shekaru 22 idan har za ta iya biyan fam miliyan 68.
Kungiyoyin Tottenham da Aston Villa na rige rigen sayen dan wasan tsakiyar Southampton James Ward-Prowse.
A Faransa kuwa Lyon na fatan za su shirya da Liverpool don dauko dan gabanta Xherdan Shaqiri mai shekaru 29.
Ita kuwa Inter Milan na shirin taya Anthony Martial na Manchester United fam miliyan 50.
Wata majiya na cewa Barcelona na bin tsohon dan wasanta Lionel Messi fam miliyan 33, a matsayin la'ada daga kudin yarjejeniyar da ya kulla da PSG.











