Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Kounde, Zouma, Haaland, Grealish, Traore, Martinez, Pogba

An wallafa

Chelsea ta soma tattaunawa da Sevilla domin yiwuwar daukar dan wasan Faransa mai shekara 22 Jules Kounde, wanda za a sayar a kan £68.4m. (Guardian)

Kazalika Blues za ta iya sanya Kurt Zouma, mai shekara 26, a matsayin wani bangare na yin musaya don daukar Kounde. (Goal)

Dan wasanBorussia Dortmund Erling Braut Haaland yana fatan rahotannin da ke alakanta dan kasar ta Norway, mai shekara 21, da shirin tafiya Chelsea a kan £150m 'jita-jita ce kawai'. (Sky Sport Germany, via Sun)

Haka kumaChelsea za ta duba yiwuwar amincewa da tayin £40m kan dan wasan Ingila Tammy Abraham, mai shekara 23. (Sky Sports)

Kyafin din Aston Villa Jack Grealish, mai shekara 25, zai yanke shawara kan makomarsa a makon gobe. Yanzu haka dan wasan na Ingila yana hutu bayan ya fafafata a gasar Euro 2020. (Mirror)

Manchester City na son soma yin tayin farko na £75m da sauran tsarabe-tsarabe kan Grealish, wanda Aston Villata yi wa kudin da suka kai £100m. (Mail)

Liverpool za ta nemi sayen dan wasan Wolves dan kasar Sifaniya Adama Traore, mai shekara 25 a kan farashin da aka rage na £30m. (Star)

Arsenal ta tuntubi Zakarun Serie A Inter Milan kan daukar dan wasan Argentina Lautaro Martinez, mai shekara 23. (Telegraph)

Dan wasan tsakiyarManchester United Paul Pogba, mai shekara 28, ba ya gaggawar yanke hukunci kan makomarsa, ko zai ci gaba da zama a Old Trafford ko ya taf wata kungiyar. Saura wata 12 kwangilar dan wasan na Faransa ta kare a United. (90min)

Fatan Ole Gunnar Solskjaer na kara 'yan wasa a tawagarsa ta Manchester United mai yiwuwa zai ta'allaka ne kan makomar Pogba da dan wasan Ingila Jesse Lingard, mai shekara 28. (Telegraph)

Dan wasan Ivory Coast Eric Bailly, mai shekara 27, zai nemi karin haske kan makomarsa a Manchester United bayan kungiyar ta cimma yarjejeniya da Real Madrid don daukar dan wasan Faransa Raphael Varane. (ESPN)