Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Raphael Varane: Man United ta amince ta dauki dan kwallon Real Madrid
Manchester United ta tabbatar da kulla yarjejeniyar sayen mai tsaron baya, Raphael Varane daga Real Madrid.
An fahimci cewar kungiyoyin biyu sun amince da cinikin kan fam miliyan 34, zai kuma kai fam miliyan 42 idan aka hada da kudin tsarabe-tsarabe.
United ta ce komai zai kammala da zarar likitoci sun auna koshin lafiyar dan wasan tawagar Faransa, idan ya amince da kunshin yarjejeniyar da za a gabatar masa.
Varane mai tsaron baya daga tsakiya mai shekara 28, ya buga wa Real Madrid wasa 360, tun bayan da ya koma kungiyar daga Lens ta Faransa a 2011.
Wanda ya lashe kofin duniya da tawagar Faransa ya ci Champions League hudu da La Liga uku a Real Madrid.
Varane, wanda ya yi wa Faransa wasa 79, zai zama na uku da Ole Gunnar Solskjaer ya dauka a bana, bayan mai tsaron raga, Tom Heaton da Jadon Sancho daga Borussia Dortmund kan fam miliyan 73.
United wadda ta amince da kudin da Real Madrid ta yi wa Varane, ta dade tana son daukar dan kwallon, wanda kwantiraginsa zai kare a karshen watan Yunin 2022 a kungiyar ta Sifaniya.
Tsohon kocin United, Sir Alex Ferguson ya kusan daukar mai tsaron bayan tun bai je Real ba, Jose Mourinho ma ya so yin zawarcin dan wasan a lokacin da yake horar da tamaula a Old Trafford.