Hazard da Courtois da Valverde sun koma atisaye a Real

An wallafa

Hazard da Courtois da Valverde sun koma Real Madrid, domin ci gaba da karbar atisaye don tunkarar kaka bana.

Real Madrid ta auna koshin lafiyar 'yan wasan uku daga baya su fara shirye-shirye atisayen kakar bana da za a fara cikin watan Agusta wato 2021/22.

Carlo Ancelotti na samun manyan 'yan wasansa da ke komawa kungiyar, don fuskantar kalubalen kakar da za a fara cikin watan Agusta, bayan da Real ta fara atisaye ranar 5 ga watan Yuli.

Tun ranar Laraba David Alaba ya fara atisaye a Real, bayan da ya koma kungiyar daga Bayern Munich a matakin wanda kwantiraginsa ya kare a kungiyar Jamus a karshen watan Yuni.

Ranar Juma'a kuwa Toni Kroos da Luka Modric da Raphael Varane da kuma Gareth Bale suka koma Real Madrid don ci gaba da atisayen.

Ana sa ran 'yan wasa takwas za su koma kungiyar don ci gaba da karbar horo a kwanan nan. Karim Benzema ya killace kansa, bayan da ya kamu da cutar korona a makon jiya.

Yayin da Eder Militao da Vinicius da kuma Casemiro ke hutu, bayan da suka buga gasar Copa America ta bana, wadda Argentina ta lashe.

Su kuwa 'yan wasa da suka hada da Marco Asensio da Dani Ceballos da Jesus Vallejo da kuma Take Kubo na wakiltar kasashensu a gasar Olympic da ake yi a Tokyo.