Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Raphael Varane: Manchester United ta yadda da farashin Real Madrid
Dan wasan Real Madrid, Raphael Varane na daf da komawa Manchester United, kan kudi da ake cewar ya kai fam miliyan 34.
Har yanzu ba a karkare kulla yarjejeniya ba - Sai dai Varane mai shekara 28, shine ya sanar da Real cewar ba zai tsawaita kwantiragin kaka daya da ta rage masa a kungiyar ba.
Ana hasashen shewar kudin dan wasan mai tsaron baya, zai kai fam miliyan 50 idan aka hada da tsarabe-tsarabe.
Wannan cinikin zai biyo bayan da Jadon Sancho ya koma Old Trafford daga Borussia Dortmund kan fam miliyan 73, wanda United ta kammala komai ranar Juma'a.
Kawo yanzu cinikayyar United ya sa ta zama kan gaba wajen kashe kudi a tsakanin abokan hamayyarta a nahiyar Turai a shirin tunkarar kakar da za a fara cikin watan Agusta.
Kocin United, Ole Gunnar Solskjaer na fatan dinke barakar bayan kungiyar, daya daga gurbin da yake da matsala, tuni kuma ya dauki dan wasan Borussia Dortmund, Jadon Sancho mai buga wasa daga gefe.
Varane ya koma Real Madrid da taka leda a 2011 daga kungiyar Faransa, mai suna Lens, wanda ya lashe La Liga uku da Champions League hudu a kungiyar Sifaniya.
Ya kuma lashe kofin duniya da Faransa a 2018, wadda ya yi wa karawa 79, ya kuma buga dukkan fafatawa hudu a Euro 2020 da suka kai zagaye na biyu.