Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Varane da Bellerin da Kane da Haaland da Jesus

An wallafa

Manchester United na dab da cimma yarjejeniya da ɗan wasan Real Madrid Raphael Varane, mai shekara 27. (Daily Mail)

Hector Bellerin ya shaida wa Arsenal cewa yana son barin ta a wannan kakar. Ɗan wasan mai shekara 26, wanda ya jima yana aiki da Mikel Arteta, na fatan komawa Inter Milan. (Metro)

Manchester City ta hakura da farautar ɗan wasan Barcelona Antoine Griezmann, mai shekara 30, sai dai za ta yi ɗamara kan ɗan wasan Borussia Dortmund asalin Norway Erling Braut Haaland, da ɗan wasanTottenham kyaftin ɗin England Harry Kane. (The Sun)

Chelsea ta shirya gabatar da tayi mai tsoka kan Haaland, a wani kokari na cimma burinta da yi wa sauran abokan hamayya fintinkau. (Daily Star)

Griezmann na iya komawa tsohuwar ƙungiyarsa Atletico Madrid, watakila a yi musaya da ɗan wasan Sifaniya mai buga tsakiya Saul Niguez, ɗan shekara 26. (Daily Express)

Mai buga wa Real Madrid tsakiya Isco a sakon Tuwitarsa - da aka goge- na nuna zai bar ƙungiyar idan kwantiraginsa ya kare, ya kuma samu tayi daga Arsenal, Tottenham Hotspur da Napoli. (Daily Mirror)

Manchester City da Wolverhampton Wanderers na zawarcin ɗan wasan Fulham Antonee Robinson. (Daily Mirror)

Juventus na farautar ɗan wasan Manchester City Gabriel Jesus, mai shekara 24. Sannan yanzu haka ta zaku kan daidaitawa da ɗan wasan Everton Moise Kean. (Tuttosport, via Daily Mail)

Tsohon ɗan wasan Manchester United Wayne Rooney ya bai wa ɗan wasan Jamaica Ravel Morrison damar atisaye da shi a Derby County. (The Sun)

Arsenal na dab da daidaitawa da Lyon' kan ɗan wasanta mai shekara 23 Houssem Aouar da ɗan wasan tsakiya Albert Sambi Lokonga, mai shekara 21 daga Anderlecht. Ɗan wasanLeicester City da England James Maddison, mai shekara 24, na cikin wadanda take hari.(The Sun)

Sabon kocin Crystal Palace Patrick Vieira na farautar mai tsaron raga Remi Matthews wanda kwangilarsa ta kare da Sunderland. (Daily Mirror)