Kano Pillars ta kai zagayen gaba a Aiteo Cup na 2021

An wallafa

Kano Pillars ta fitar da Smart City daga Aiteo Cup na bana, bayan da ta yi nasara da ci 4-2 a fafatawar da suka yi ranar Laraba.

Pillars din ta ci kwallo biyu tun kan hutu ta hannun Ebuka da wadda Yanki ya zura a raga a karawar da suka yi a filin wasa da ke Lokoja.

Sai masu gida ta kara daya tun farkon da suka koma zagaye na biyu ta hannun Okon, sannan Nwagua ya ci na hudu daf da za a tashi daga karawar.

Sai dai kuma Smart City, wadda take daga jihar Legas ta zare kwallo biyu a wasan.

Da wannan sakamakon Pillars wadda ke rike da Aiteo Cup tun 2019, ta kai karawar kungiyoyi 16 da za su fafata a wasannin gaba a gasar bana.

A watan Yulin 2019 Kano Pillars ta doke Niger Tornadoes ta lashe Aiteo Cup a karon farko tun bayan shekara 29.

Cutar korona ce ta kawo tsaikon da ba a ci gaba da buga gasar ba a bara da ta kai Pillars ta wakilci Najeria a gasar Confederation Cup ta Afirka ganin ita ce ke rike da kofin.

Pillars tana mataki na uku a teburin Premier na bana da maki 55, iri daya da wanda Nasarawa United ta hada mai zaune a gurbi na biyu.

Har yanzu Akwa United ce ta daya mai maki 57, bayan da aka karkare wasannin maki na 31 a gasar ta Firimiyar Najeriya.