Pillars ta ragargaji Nasarawa United

An wallafa

Kano Pillars ta doke Nasarawa United ta ci 3-0 a wasan mako na shida a gasar cin kofin Firimiyar Nigeria da suka fafata a Sani Abacha da ke kofar Mata a Kano, Nigeria.

Pillars ta ci kwallayen ne tun kan a je hutu ta hannun Adamu Hassan wanda ya ci biyu a karawar, sannan Chinedu Sunday ya zura daya a raga.

Wannan shi ne wasa na biyu da kocin Pillars Ibrahim Musa ya ja ragamar kungiyar tun bayan da ya sake komawa kan aikin koci, bayan da aka sallame shi a bara.

Kawo yanzu Pillars ta ci wasa biyu da canjaras biyu aka doke ta karawa biyu, tana da maki takwas kenan kawo yanzu.

Sauran sakamakon wasannin mako na shida:

  • MFM 1-0 Wikki
  • Enyimba 2-0 Rivers Utd
  • Sunshine Stars 2-1 Remo Stars
  • Katsina Utd 3-1 Tornadoes
  • El-Kanemi 2-1 Yobe Stars
  • Akwa Utd 3-0 Go Round
  • Gombe Utd 0-0 Plateau Utd
  • Heartland 3-2 Kada Stars
  • FCIU 1-2 Abia Warriors