Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kano Pillars na fatan daukar Firimiyar Najeriya
Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars na fatan lashe gasar lig ta Firimiyar Najeriya ta hanyar daukar kofin Super six wanda ake yi a birnin Legas.
Pillars, wacce take matsayi na biyu a tebur da maki takwas za ta fafata da Lobi Stars, yayin da Enyimba, wacce mataki na daya da maki tara za ta kara da Akwa United.
Kano Pillars na bukatar ta doke Lobi Stars, sannan kuma ka da Enyimba ta yi nasara a kan Akwa United.
Sai dai wasan Enyimba za a fara yi kafin na Pillars.
Wasu masu sharhi na ganin zai yi wuya Pillars ta kai labari domin damar ba a hannunta take ba.
A baya Pillars ce take kan gaba a rebur kafin ta yi canjaras da Enugu Rangers, abin da ya bai wa Enyimba damar darewa sama.
Sai dai wasu magoyan Pillars din sun shaida wa BBC cewa suna da kwarin gwiwar lashe gasar.
Duk kungiyar da ta zo ta daya ita ce za ta lashe kofin, sannan ta samu tikitin zuwa gasar cin kofin zakarun Afirka tare da ta biyu, ita kuma ta uku za ta je gasar Confederations Cup.
Wasannin da za a fafata ranar Laraba
- FC Ifeanyi Ubah da Enugu Rangers
- Enyimba da Akwa United
- Lobi Stars da Kano Pillars