Kasuwar ƴan wasa: Makomar Grealish, Ronaldo, Rabiot, Xhaka, Ramsdale

An wallafa

Aston Villa na fatan yi wa kyaftin dinta Jack Grealish, mai shekara 25, tayin sabuwar kwantiragin fam 150,000 a duk mako, bayan da Manchester City ke son daukar dan wasan tawagar Ingila. (Telegraph - subscription required)

Juventus na fatan Cristiano Ronaldo, mai shekara 36, zai yanke hukuncin makomarsa a fanni tamaula, bayan da aka fitar da Portugal daga gasar cin kofin nahiyar Turai, wato Euro 2020. Yarjejeniyar dan wasan da ya lashe Ballon d'Or biyar za ta kare da kungiyar da ke buga gasar Serie A zuwa karshen kakar 2022. (Tuttosport - in Italian)

Manchester United ta tura jami'anta domin su duba kwarewar dan wasan tawagar Faransa mai taka leda a Juventus, Adrien Rabiot, mai shekara 26, bayan da Switzerland ta yi waje da mai rike da kofin duniya daga gasar cin kofin nahiyar Turai ranar Litinin. (Star)

Juventus ta shiga sahun wadanda ke son sayen dan kwallon Arsenal, Granit Xhaka, bayan da Roma ma ke son daukar dan wasan mai shekara 28 kyaftin din tawagar Switzerland. (Calciomercato - in Italian)

Crystal Palace da Southampton da kuma Norwich City na fatan kulla yarjejeniyar daukar dan wasan Borussia Dortmund mai shekara 29, Thomas Delaney, wanda yarjejeniyarsa za ta kare a karshen kakar 2022. (Sky Germany - in German)

Ana sa ran dan wasan tawagar Ingila, mai shekara 24, Jack Harrison, zai kamala komawa Leeds United aa makon nan, bayan da ya buga wasannin aro daga Manchester City tsawon kaka uku. (Manchester Evening News)

Haka kuma ana sa ran Leeds za ta kammala cinikin dan kwallon Barcelona, Junior Firpo, mai shekara 24, duk da cewar kungiyoyin da ke buga Premier League da Serie A na son daukar dan wasan tawagar Sifaniya. (Goal)

Ana sa ran Arsenal za ta mika bukatar daukar mai tsaron ragar Sheffield United, Aaron Ramsdale, mai shekara 23, da zarar ya koma gida, idan ya gama buga wa tawagar Ingila Euro 2020. (Sheffield Star)

Aston Villa na sha'awar daukar aron dan wasan Manchester United mai tsaron baya daga tsakiya Axel Tuanzebe don buga mata tamaula a kakar 2021-22 bayan da dan kwallon mai shekara 23 ya taba yi wa Villa wasannin aro har karo biyu a Villa Park. (Football Insider)

Haka kuma Villa ta ci gaba da nuna sha'awar sayen dan wasan Chelsea, Tammy Abraham, mai shekara 23, wanda aka yi wa farashin fam miliyan 40, wanda ya yi wa West Ham United tsada matuka. (Eurosport)