Manchester United ta dauki Jadon Sancho

An wallafa

Manchester United ta amince da kudin da Borussia Dortmund ta gindaya, domin daukar dan wasan tawagar Ingila, Jadon Sancho.

BBC ta fahimci cewar United za ta biya Dortmund fam miliyan 73 kudin dan wasan mai shekara 21, wanda ya koma Jamus da taka leda daga Manchester City a 2017.

Wannan labari ne mai faranta ran koci Ole Gunnar Solskjaer, wanda ke son bunkasa United, don taka rawar gani a kakar da zamu shiga.

United ta yi ta biyu a gasar Premier League, wadda Manchester City ta lashe kofi na uku cikin shekara hudu, kuma United ta kai wasan karshe a Europa League da Villareal ta lashe.

Tun farko kocin United ya fayyace gurbi hudu a kungiyar da yake son toshe baraka da suka hada da gefen hagu daga gaba da mai tsaron baya daga tsakiya da mai wasa daga tsakiya da mai cin kwallaye.

Tun a bara United ta yi niyyar sayen dan wasan, amma Borussia Dortmund taki amincewa ya bar buga gasar Bundesliga.

Da wannan cinikin zai zama dan Ingila mafi tsada a duniya, bayan Harry Maguire, wanda ya koma United daga Leicester City kan fam miliyan 80 a Agustan 2019.

Sancho ya ci kwallo 50 ya kuma bayar da 57 aka zura a raga a karawa 137 da ya yi wa Dortmund, wanda ya ci biyu a German Cup wasan karshe, inda mai buga gasar Bundesliga ta doke RB Leipzig a 4-1 a cikin watan Mayu.

Dan kwallon ya buga wa tawagar Ingila wasa 20 tun da ya fara buga mata tamaula a 2018, ya kuma ci kwallo uku, yana cikin masu buga mata gasar Turai ta Euro 2020.