Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Saura maki daya tsakanin Akwa United da Pillars
Kungiyar Kano Pillars ta yi nasarar doke FC Ifeanyi Ubah da ci 1-0 a wasan mako na 29 da suka kara a gasar Firimiyar Najeriya ranar Lahadi.
Pillars din da ake kira masu gida ta ci kwallon ta hannun David Ebuka tun kan hutu, kuma hakan ne ya bai wa kungiyar ta Kano maki ukun da take bukata.
Da wannan sakamakon Pillars din tana nan a matakinta na uku da maki daya tal tsakaninta da Akwa United ta daya a kan teburi, wadda ta yi rashin nasara da ci 1-0 a jihar Katsina ranar Lahadin.
Nasarawa United wadda ta doke Rivers United ta ci gaba da zama ta biyu a kan teburi mai maki 52, iri daya da wanda Pillars take da shi bayan wasa mako na 29.
Bambanci tsakanin ta biyu da ta uku shi ne, Nasarawa ta zura kwallo 39 a raga aka ci ta 27, kenan da rarar 12, ita kuwa Pillars 30 ta ci aka zura mata 22 a raga mai rara takwas kenan.
Wasu sakamakon wasannin mako na 29 da aka buga ranar Lahadi:
- Wikki Tourists 1 - 0 Lobi Stars
- Katsina United 1 - 0 Akwa United
- Nasarawa United 2 - 1 Rivers United
- Warri Wolves 0 - 1 Enugu Rangers International
- Abia Warriors 0 - 1 Dakkada
- Kada City 1 - 0 Sunshine Stars
- Heartland 2 - 0 Mountain Of Fire And Miracles