Ronald Koeman zai ci gaba da horar da Barcelona

Asalin hoton, Getty Images
Kocin Barcelona, Ronald Koeman zai ci gaba da jan ragamar kungiyar a kaka mai zuwa, bayan da ya amince da tsawaita yarjejeniyarsa a Camp Nou.
Shugaban kungiyar, Joan Laporta ne ya sanar da hakan ranar Alhamis cewar sun cimma kwantiragi tsakaninsu da kocin dan kasar Netherlands.
Koeman ya koma Camp Nou da horar da tamaula cikin watan Agusta karkashin tsohon shugaba, Josep Mario Bartomeu, wanda ya yi ritaya daga aikin.
Barcelona wadda ta lashe Copa del Rey a bana ta karkare La Liga a mataki na uku da hakan ya sa ake cewar kungiyar na neman kocin da za ta dauka.
A watan jiya Laporta ya fayyace karshen aikin kocin ya kare, kuma bai mara baya kan yadda ya gudanar da aikinsa a Camp Nou ba, amma ya ce za su yi nazari a lokacin.
Daga baya ya kawo karshen rade-radi kan makomar Koeman, bayan da ya sanar cewa kungiyar za ta fayyace idan zai ci gaba da aiki ko akasin hakan.
''Bayan da muka yi nazarai kan yadda Koeman ya ja ragamar Barcelona da rawar da ya taka, mun amince Koeman ya ci gaba da aiki kan yarjejeniyar da aka kulla da shi tun farko,'' in ji Laporta a lokacin da ya sanar da manema labarai.











